Taron masan bincike a harkar kiwon lafiyar bil’adama, sun kirkiri wani sabon mashin, da za’a dinga amfani da shi wajen gwajin jinin mutun, don tantance ko mutun na dauke da kwayoyin cutar kansa. Hasali ma wannan mashin din, zai bayyanar da bangaren da cutar take a cikin jikin mutun.
Hakan na nuni da cewar ana gabda kawo karshen barnar da cutar kansa, keyi a jikin dan’adam. Sabon mashin din nada karfin gano inda cuta ke zaune a cikin jikin mutun, kuma za’a yi amfani da mashin din wajen kona cutar cikin gaggawa.
Masana a jami’ar California, sun bayyanar da ayyuka da mashin din zai dinga yi, sun hada da duba jinin mutu da bayyanar da jinsin da mutun ya fito, zai bayyanar da tsatson mutun. Za’a iya amfani da wannan mashin din wajen tabbatar da cutar kansa ko dai a hanta, huhu, kwakwalwa, da duk wani bangaren jiki da take kamawa.