Wani sabon bincike da taron masana suka fitar, na nuni da cewar matasa masu shekaru 19-32, na shiga cikin matsalolin rayuwa a sanadiyar yawan amfani da kafofin yanar gizo. Binciken dai ya duba yadda matasa kanyi amfani, da kafofin sadarwar zamani wanda daga bisani, sukan fuskanci turjiya a sha’anonin rayuwar su ta yau da kullun.
Masanan sun dauki matasa 1,787 don gwaji akan harkar da ta shafi rayuwar su ta yau da kullun, da yadda suk gudanar da mu’amalolin su. Binciken ya bayyanar da cewar, duk matsashi da kan kwashe sama da awowi biyu a yini, wajen shiga kafofi yanar gizo, da suka hada da shafufukan Facebook, YouTube, Instagram, Snapchat, Twitter da LinkedIn, haka da makamantan su.
Matasan suna iya kamuwa da wata cutar kadaici, wanda zasu kasance basu da sha’awar tarayya da mutane. Duk kuma matasan da sukan ziyarci shafufuka da suka kai sau 58 a sati, to zasu iya kamuwa da irin wannan cutar, sai dai ba dole bane ta iya kaiwa babban mataki.
Jaridar masana binciken kiwon lafiya da’adam ta jami’ar Pittsbugh dake kasar Amurka, sun bayyanar da cutar kadaici, a matsayin cuta da takan iya shafar kwakwalwar mutun, daga bisani kuma tana iya haifar da matsaloli ga lafiya mutu.
Don haka yana da matukar muhimmanci idan mutane zasu kwatanta amfani da yanar gizo, wajen karfafa mu’amalar su da mutane, fiye da lokacin da sukan kashe wajen ziyartar yanar gizo.