Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Musulma 'Yar Asalin Nahiyar Afrika, A Matsayin 'Yar-Majalisar!


Ilhan Omar, Zababbiyar 'Yar-Majalisar Dokokin Jihar Minnesota.
Ilhan Omar, Zababbiyar 'Yar-Majalisar Dokokin Jihar Minnesota.

A karon farko an rantsar da mace ‘yar-asalin kasar Somalia, a matsayin ‘yar majalisar dokokin jihar Minnesota, ta kasar Amurka. “Ilhan Omar” ta zama mace ta farko kuma Musulma, dake da asali daga nahiyar Afrika, a matsayin zababbiyar ‘yar-majalisar dokokin jihar Minnesota.

A shekarar da ta gabata an gabatar da zabe mai ban al’ajabi, da rudani a kasar Amurka. Zaben dai ya maida hankali ne, akan bangaranci na addinin, da bakin haure. Duk da zafafan yakin neman zabe a tsakanin ‘yan-siyasa masu ra’ayin korar Musulmai daga kasar Amurka, zuwa masu akidar barin su.

Hakan dai bai zama tsaiko baga Ilhan, domin kuwa ta samu kuri’u masu yawa daga turawa farare, a lokacin zaben ta na matsayin ‘yar-majalisar dokoki. Wanda hakan zai bata damar shiga a dama da ita acikin siyasar Jihar Minnesota.

A karon farko anyi amfani da Al-Qur’ani mai tsarki, a harabar majalisar dokokin jihar Minnesota, inda aka bama zababbiyar ‘yar-majalisar Ilhan Omar, don rantsewa da dokokin jihar da daukar alkawalin yin aiki tsakanin ta da Allah.

‘Yan’uwa da abokan arziki sun halarci taron, inda suka bayyanar da goyon bayan su da fatar alkhairi ga ‘yar-majalisar. Haka sauran mazauna yankin da zata wakilta, suna mata kyakyawar fata da addu’ar Allah, yasa suyi nasara baki daya.

Haka suna fatar ganin canji, a tsarin aikin ta, kasancewar itace mace musulma, ta farko da ta taba rike wannan matsayi, don haka suna sa ido don ganin irin rawar da zata taka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG