Shekarar 2016, shekara ce mai dauke da abubuwa da baza’a taba mantawa da suba, a tarihin karni na ashirin da daya 21. A karon farko da yanar gizo ta taka muhimmiyar rawa wajen ruruta labaran karya da basu da makama.
Kana ‘yan kutse sunyi amfani da kafofin yanar gizo, wajen satar bayanan sirri, ba kawai na mutane ba, harma da na manyan kamfanoni a fadin duniya. Kamfanin Yahoo, sun fuskanci makamanciyar wannan matsalar, inda aka samu damar shiga cikin asusun kimanin fiye da mutane billiyan daya a duniya.
Haka wani babban asibiti dake kasar Amurka, sun fukanci matsalar satar bayanai da aka dauki bayanan, marasa lafiya na asibitin. Da dama daga cikin kamfanonin nan sun kashe zunzurutun kudade wajen shawo kan matsalar.
Wayoyin hannu da dama a fadin duniya sun fuskanci barazana, wajen aika wasu cututtuka dakan iya cutar da wayoyin “Virus” Kasar India itace kasa da tafi kwararan matakan tsaro wajen ajiyar bayanan sitrri na kamfanoni da mutane a fadin duniya.
Za'a iya cewa wannan shekarace da akayi amfani da yanar gizo ta hanyoyi da dama, wasu sun taimaka matuka wasu kuwa, sun wargaza wasu tsare-tsaren mutane da dama. Ana kara kira da jama'a su maida hankali wajen amfani da kafofin ta yadda zai taimaka matuka ga cigaban kasa da al'umah.