Babban shahararren kamfanin kasuwar yanar gizo “Amazon” sun kafa tarihi. A karon farko kamfanin sun cinma nasara wajen amfani da mutun mutumi don kai sako gidajen mutane, cikin gaggawa.
Kamfanin Amazon, yazo na daya a cikin jerin kamfanoni a fadin duniya, da kanyi harkar siye-da-siyarwa duk a yanar gizo, batare da shiga kasuwa ba. Yanzu haka dai kamfanin sun kammala shirye-shirye, don bude wata sabuwar cibiya wadda zasu dinga amfani da na’urar drone wajen kai sako gidanje abokan hurdar su.
Mafi akasarin mutane a kasashe da suka cigaba, sukan yi amfani da yanar gizo wajen siyan kowane irin abun suke da bukata, a rayuwar yau da kullun. Wannan wata damace da za’a saukaka aika kaya da mutane suka siya cikin gaggawa.
A duk lokacin da mutun yayi siyayyar shi ta hannun kamfanin, bashi da bukatar sai yajira na tsawon kwanki, domin kuwa yanzu haka Amazon zasu dinga amfani da Drone, wajen kai sako cikin lokaci da bama mutane damar siyan abu a kowane lokaci.