Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Matan Nan Biyu Masu Nadar Bayanan Attajiran Najeriya Sun Bada Hakuri


Jyoti da Kiran Matharoo
Jyoti da Kiran Matharoo

'Yan matan nan biyu 'yan uwan juna 'yan kasar Canada Jyoti da Kiran Matharoo, da ake zargi da amfani da surarsu ta hanyar yanar gizo wajen yaudara da kuma tilasta attajiran Nigeria su basu kudi sun bawa babban Attajirin nan femi otedola hakuri.

Ance 'yan matan biyu suna nadar tattaunawar batsa da wasu manya manyan mutanen da sukayi hulda da su wajen tsorata mutanen su basu dubban daloli don su sakaya sunayensu ko kuma su fuskanci fallasa.

Ana zargin su da hada baki da babatunde ayebode mai dandalin internet dinnan mai suna naijajestlive wajen gudanar da wannan aika aikikar.

A wani faifain gidan video da gidan talabijin na sahara ya fitar jiya Alhaaamis yan matan sun nemi afuwa daga otedola saboda yunkurin tsorata shi don ya basu kudi.suka ce ba kan tilas akayi faifan videon ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG