Jamila Kabiru Mado, wata matashiya' yar jihar Kano da ta karanci kimiyya da fasaha, ta ce tana gudanar da binciken ne na wani sinadari da ake sanyawa a cikin lemuka ko madara na gwangwani da kamfanoni ke yi.
Ta ce lokacin da ta fara karatu ta so ta karanci liktanci amma hakkar ta bata cimma ruwa ba, bayan ta kamala kwas din da ta fara da farko sai ta dawo jami’ar Bayero inda ta karanci Chemistry, duka a layin kimiyya da fasaha.
Bayan ta fara karantun wanda ya fi maida hankali ga gwaje-gwaje, bayan digirinta na farko sai koma makaranta domin yin karatun gaba da digiri, a inda ta fara binciken wannan sinadarin, na binciken yawan sinanrin Salicylic acid domin sanin adadin da ya kamata kamfanonin ya kamata su sa.
Ta ce babban burin dai a yanzu da ta kamala digirin ta na biyu ta na so ta koma makaranta domin zama Dakta wato digiri na uku, ta kara da cewa yanzu mata sun waye suna kokartawa don kada a barsu a baya.