Taron kwararrun likitoci a kasar “Vietnam” sun gabatar da tiyata a cikin-cikin wani mutun mai shekaru hamsin da hudu 54. Kimanin shekaru goma sha takwas 18, da suka gabata anyima mutumin aiki a cikin shi, wanda aka bar Almakashi a cikin shi.
Mr. Ma, dai ya samu hadarin mota, wanda aka kai shi asibiti, biyo bayan daukar hoto da akayi a cikin shi, an samu ganin Almakashi da ya kwashe tsawon shekaru goma sha takwas 18, wanda bai san da almakashin a cikin shi ba.
Tun a shekarar 1998, da aka gudanar da wani aiki a cikin-cikin shi, aka bar almakashin. Kimanin tsawon almakashin ya kai tsawon mitoci goma sha biyar. Ya bayyanar da cewar bai taba samun wani ciwo a sandiyar almakashin dake cikin-cikin shi ba.
Ministan lafiya na kasar ya umurci asibitin “Bac General Hospital” da suyi bincike don gano likitan da yayi ma Mr. Ma, aiki a shekarar 1998, don hukunta shi. Ana dai sa ran Mr. Ma, zai koma gida a sati mai zuwa idan Allah ya kai rai.