A cikin shirye-shirye da ake na tunkarar wasannin Olympic, mai take “Rio 2016” da za’a fara a wannan satin idan Allah, ya kaimu ranar Juma’a mai zuwa. Hukumomi a kasar Brazil, sun bayyanar da irin shirin da sukayi don ganin an samu gudanar da wasanni cikin kayatarwa da tsaro.
Wasan dai a bana, zai samu halartar ‘yan wasa da dama da zasu kara a wasannin iri daban daban a fadin duniya. A yanzu haka dai an samar da jami’an tsaro na ‘yan sanda sama da dubu dari da talatin 130,000. Duk don ganin an samu tsaro da walwalar ‘yan wasa da masu kallo.
A cikin irin tsare tsare da aka tanadar, an samar da wata na’urar daukan hoto mai suna “eye-in-the-sky” wadda kyamarori ne da aka rataye su a sararin samaniya. Zasu dinga bada rahoton mai ke gudana a bakidaya harabar da ake gudanar da wasannin.
An kirkiri wadannan kyamarorin ne don magance matsalar rashin tsaro, wanda an gwada aikin wadannan kyamarorin a kasashen Iraq, da Afghanistan, kyamarorin nada karfin daukar hoto komi nisan shi zuwa kusa.