Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin "UBER" Zasu Samar Da Taswirar Duniya Ta Jeka Da Kanka!


Kamfanin Tasi
Kamfanin Tasi

A irin cigaba da aka samu a kasashen duniya da suka cigaba, musamman a fanin kimiyya da fasaha. Yawancin motocin zamani na amfani da wata na’ura da ake kira “GPS” wanda takan nuna ma mutun hanya, da gayama mutun ko karfe nawa zai isa duk inda yake da bukatar zuwa, haka zata gaya ma mutun yanayin zafi da na sanyi, kana idan akwai hadari a kan hanya duk zata sanar da matukin motar.

Wani shahararren kamfanin Tasi mai suna “UBER” sun ware kimanin dallar Amurka milliyan dari biyar $500M don samar da wannan tsarin da zai nunama mutun hanya a fadin duniya. Abu da kawai mutun yake bukata shine ya samu wannan na’urar ya saka cikin motar shi, kana ya rubuta adireshin gidan da yake son zuwa a koina wannan na’urar zata nuna mishi hanya batare da mutun yayi tambaya ba.

Babban yunkurin su shine, idan har suka kammala wannan aikin, motoci masu tuka kansu, zasu samu damar kaiwa da komowa batare da samun hadari ko wata matsala ba. A wani rahoto da aka fitar mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin Mr. Brian McClendon, ya bayyanar da yunkurin su na samar da wannan taswirar wadda zatafi karfin ta kamfanin Google. Nan bada jimawa ba zasu bada damar saka wadannan motocin masu tuka kansu a kan tituna a fadin duniya.

Yadda suke gudanar da aikin su, shine idan mutun yana da mota, sai su bashi damar daukar fasinjoji wanda mutun zai biya kudin motar ta hannun kamfanin, shi kuwa a karshen wata sai kamfanin su bashi kudin aikin shi su kuwa su cire nasu kason. Idan aka kammala wannan aikin za'a kai lokacin da mutun bashi da bukatar tuka mota da kanshi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG