Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta kashe wani shugaban mayakan ISIS a Iraqi


Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter
Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter

Harin da Amurka ta kai da jirgin nan mara matuki ya kashe daya cikin shugabannin ISIS a kasar Iraqi

A jiya Lahadi sojojin Amurka suka ce daya daga cikin jiragen yakinsu marar matuki a Iraki ya kashe daya wani mayakin ISIS din da suka yi amannar cewa shine ke da alhakin kai harin makami mai linzami a watan da ya gabata wanda ya kashe sojan ruwan Amurka.

Kakakin rundunar sojin Amurka da ke yakar ‘yan ta’addar Steve Warren ne ya bayyana haka. Ya kara da cewa, harin da jirgin ya kai ya kashe Jasim Khadijah hade da wasu mayakansu guda 5, haka kuma Jasim tsohon jami’in Iraki ne kuma gwani a fannin makamin roka.

Warren yace, mutumin shine ya sarrafa makamin mai linzami da yayi sanadiyyar mutuwar sojan Amurkan Sergent Louis Cardin tare da raunata wasu sojojin ruwan guda 8 a sansanin makaman yaki da ke Makhmur a Arewacin Iraki.

Cardin dai shine jami’in sojan Amurka na 2 da ya rasa ransa a filin daga tun bayan kaddamar da yakin da Amurka ke yin a kokarin dakile ‘yan ta’addar ISIS wanda aka fara tun na shekarar 2014.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG