Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai sarafawa ISIS bamabamai ya mutu a harin Brussels


Mutane biyun ada suka kai hari Belgium da su ma suka mutu
Mutane biyun ada suka kai hari Belgium da su ma suka mutu

Jami’an leken asiri sunce matashin nan mai shekaru 25 me kera boma bomai dan kungiyar ISIS, wanda ke da hannu a harin da aka kai birnin Paris cikin watan Nuwamba, na daya daga cikin mutane biyun da suka kai harin kunar bakin wake a filin saukar jiragen sama na Brussels.

Najim Laachraoui, haifaffen kasar Morocco ne wanda ya girma a Brussels, hukumomi sun bayyana shi cikin mutanen da suka shirya harin Paris, bayan da aka gano sinadarin kwayar halittarsa jikin rigar da masu kunar bakin waken suka saka. Haka kuma an kara samun sinadarin halittarsa a gidan da jami’ai suka yi imanin an hada boma boman da aka yi amfani da su.

A jiya Laraba ne shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace, an gano dan kunar bakin wake na biyun, shine wanda a baya aka kama shi a Turkiyya kuma aka mayar da shi Turai aka kuma sake shi watanni 8 da suka gabata.

Erdogan yace gwamnatinsa ta gargadi hukumomin Brussels akan Ibrahim el-Bakraoui, wanda aka kama a kudancin Turkiyya a yayin da yake kokarin tsallakawa zuwa Siriya. Shugaban na Turkiyya yace tun watan Yulin shekarar da ta gabata aka tura shi Turai, amma duk da gargadin da aka yiwa hukumomin sai da suka sake shi.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG