Jami’an Ma’aikatar sun sanar da matakin a ranar Talata, inda suka tayar da ayar tambaya kan yadda hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da ta saba gudanarwa.
Sama da mutum 250 ne suka kamu da cutar kyanda a Yammacin Texas da New Mexico a Amurka, kana wasu mutum biyu da ba su yi allurar rigakafin cutar kyanda ba sun mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Bayan kusan sa’o’i takwas ana tattaunawa, Ukraine ta sanar da shirinta na amincewa da shawarar Amurka na tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30, a yakin da take yi da Rasha, yayin da take jiran amincewar Kremlin.
A ranar Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin murkushe masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a manyan makarantun Amurka, inda ya ce, tsare Mahmoud Khalil wani jagoran masu bore a jami’ar Columbia dake New York somi ne, a dimbin kamen dake tafe.
Sakataran Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Litinin cewa, Amurka na fatan ganin an warware batun dakatar da taimako agaji ga Ukraine, yayin tattaunawa a yau Talata tare da jami’an Ukraine a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.
Gwamnatin Trump ta fito da wata sabuwar manhaja da zata ba baki 'yan cirani dake zaune a Amurka ba bisa ka’ida ba damar maida kansu gida, maimaimakon fuskantar kamu da tsarewa, wani abu dake dorawa kan shirin shugaba Donald Trump na maida bakin haure kasashen su.
Boehler ya shaida wa shirin ‘State of the Union’ na gidana talabijin din CNN cewa “Ina tsammanin za a samu yarjejeniya muddin aka sako dukkan wadanda aka yi garkuwa da su.”
Trump ya sanar a yayin wata hira da Shirin labaran Kasuwanci na Fox da aka nada ranar Alhamis kana aka yada da safiyar ranar Juma’a cewa ya aika wata wasika ga Ali Khamenei, yana fada wa shugaban addinin na Iran cewa “Zai yiwa Iran kyau idan ta bada hadin kai ga tattaunawar nukiliya.
Shirin saka harajin har ila yau ya yi sanadiyyar faduwar farashin hannayen jari na tsawon kwanaki tare da kawo cikas ga dangantakar Amurka da kawayenta da suka dade da kuma manyan abokan cinikiyyarta biyu.
"Abin da kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi suka tilasta mu yi shi ne yin amfani da dukkan albarkatun sojojin Amurka domin aiwatar da tsauraran matakan kare iyaka." In ji Vance.
Ratcliffe yace dakatarwar a fagen daga dana musayar bayanan sirri ta wucin gadi ce, kuma yana sa ran cewar Amurka za ta koma aiki kafada da kafada tsakaninta da Ukraine a nan gaba.
A ranar 31 ga watan Disamban 2021, Amurka ta janye ragowar dakarunta daga Afghanistan, inda ta dakatar da rudanin debe dubun dubatar mutanen kasar da suka yiwa tashar jiragen saman birnin Kabul tsinke da nufin hawa jirgin da zai fitar dasu daga kasar.
Domin Kari
No media source currently available