Shugabanni a bangarori da dama a nahiyar Turai sun sha alawashin tsayawa tare da Ukraine bayan ganawa tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a fadar White House ta rikide ta koma zazzafar musayar yawu a ranar Juma’a, inda Trump ya kira Zelenskyy da mara da'a.
Shugabanin Amurka da Ukraine sun gaza cimma matsaya game da yarjejeniyar ma'adinai yayin da zukata suka hasala game da mamayar Rasha da kuma makomar tattaunawar.
“Saka harajin ya zama wajibi, saboda kasashe da dama ba sa kyauta mana, ciki har da kawayenmu da abokan hamayyarmu.” In ji Trump.
Tunda fari Trump ya sanar - amma ya dakatar daga bisani - da batun kakaba harajin kaso 25 cikin 100 a kan kayayyakin da ake shigowa da su Amurka daga kasashen Canada da Mexico a watan da muke ciki sakamakon matsalar bakin haure da muguwar kwayar nan ta Fentanyl,
Yarjejeniyar ta bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da bayar da “tallafin kudi domin samar da wata Ukraine mai zaman lafiya da wadata ta fuskar tattalin arziki.”
Attajirin wanda tsohon mai harkar cinikin gidaje ne yace za a tantance dukkanin mutanen da suka nemi sayen sabbin katunan kafin a sayar musu.
Ukraine da Amurka sun cimma matsaya kan tsarin kulla yarjejeniyar tattalin arziki mai fadi da za ta hada da samun damar mallakar ma’adanan karkashin kasa da babu su a duniya, in ji wasu manyan jami’ain Ukraine uku a ranar Talata.
A ranar Litinin shugaba Donald Trump ya ce, yana gab da cimma kulla yarjejeniya da Ukraine da kuma Rasha domin kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine, bayan yini guda da aka kwashe ana ganawa a fadar White House da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Macron na fatan sauya ra’ayin Trump a bikin zagayowar shekara ta 3 da fara yakin Ukraine domin shigar da shugabannin Turai cikin tattaunawar Rasha da Amurka.
Gwamnan jihar California Gavin Newsom ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta amince da tallafin kusan dala biliyan $40 domin taimakawa yankin Los Angeles ta farfado daga mummunar gobarar dajin da ta afku a watan Janairun bara, wanda a cewarsa zai iya zama bala’I mafi tsada a tarihin Amurka.
Trump ya ce "Wannan babban al’amari ne kuma su ‘yan Ukraine suna bukatar haka, kana hakan zai sa mu kansance a cikin kasar," inda ya kara da cewa "Zamu maido da kudadenmu." Ya ce wannan wata jarjejeniya ce da ya kamata a kulla tun kafin ya karbi ragamar mulki.
Jirgin saman da ya daukesu ya tashi ne daga garin San Diego, na jihar California, inda ya sauka a wani sansani dake kusa da tashar jiragen saman kasa da kasa ta Juan Santamaria.
Domin Kari
No media source currently available