A ranar Juma’a Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana alamar daukar matakin soja a kan kasar Iran, sai dai idan kasar ta amince da wata sabuwar yarjejeniya da za ta dakile shirinta na nukiliya da ke ci gaba cikin gaggawa.
“Ana Shirin ganin abubuwa masu daukar hankali a cikin kwanakin dake tafe. Shine kawai abin da zan iya fada muku," shugaban yana fada wa manema labarai a ranar Juma’a a ofishinsa na Oval.
Trump ya sanar a yayin wata hira da Shirin labaran Kasuwanci na Fox da aka nada ranar Alhamis kana aka yada da safiyar Juma’a cewa ya aika wata wasika ga Ali Khamenei, yana fada wa shugaban addinin na Iran cewa “Zai yiwa Iran kyau idan ta bada hadin kai ga tattaunawar nukiliya.
“Idan kuwa matakin soja suke so, to lallai ba za su ji da dadi ba,” yana fada yayin hirar.
Trump ya ce Amurka ta kai lokacin daukar matakin karshe a kan Iran, kana ya nuna alamar sa ido akan rijiyoyin man kasar.
“Muna da batutuwa da Iran kuma wani abu zai faru nan ba da jimawa ba, cikin sauri,” in ji shi. “Ni dai ina cewa na fi son ganin yarjejeniyar zaman lafiya fiye da dayan, amma dayan zai magance matsalar."
Yarjejeniyar da Trump ke magana akai za ta maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla a shekarar 2015, wadda aka fi sani a taurance da “Joint Comprehensive Plan of Action” (JCPOA) kan Iran.
JCPOA wata muhimmiyar manufar harkokin waje ne da aka cimma a lokacin mulkin tsohon shugaba Barack Obama. A cikin 2018, a lokacin wa'adin mulkinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar.
Dandalin Mu Tattauna