Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan California Ya Nemi Majalisa Ta Amince Da Tallafin Kusan $40B Ga Wadanda Gobarar Los Angeles Ta Shafa


Gwamnan California Gavin Newsom
Gwamnan California Gavin Newsom

Gwamnan jihar California Gavin Newsom ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta amince da tallafin kusan dala biliyan $40 domin taimakawa yankin Los Angeles ta farfado daga mummunar gobarar dajin da ta afku a watan Janairun bara, wanda a cewarsa zai iya zama bala’I mafi tsada a tarihin Amurka.

Newsom ya aika da wata wasika a ranar Juma’a da gabata yana neman taimakon ‘yan majalisa ciki har da Kakakin Majalisa Mike Johnson da dan Majalisa Tom Cole na Republican, shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisa.

Newsom ya rubuta cewa “Los Angeles tana daya daga cikin wurare masu wadatar tattalin arziki a duniya, amma za ta iya farfadowa da bunkasa tare da tallafi daga gwamnatin tarayya yayin da take murmurewa daga wannan bala’i da ba’a taba ganin irinsa ba.”

An kiyasta jumular asarar dukiya daga gobarar da ta zarce dala bliyan $250, yayin da asarar gidaje daga gobarar Palisades da Eaton da aka yi hasashen za ta kai dala biliyan $30, a cewar wani sharhin da jaridan Los Angeles Times ta yi.

Fiye da gine-gine 16,200 ne suka lalace yayin da wutar ta mamaye Pacific Palisades, Malibu, Pasadena da kuma Altadena.

Newsom ya sha alwashin cewa za’a yi amfani da kudaden ne wajen sake gina gidaje, ababen more rayuwa, kasuwanci, makarantu, coci-coci da kuma cibiyoyin kiwon lafiya, sannan da tallafawa bukatun mutanen da bala’in ya shafa.

Newsom ya rubuta cewa “Babu kuskure, Los Angeles za ta yi amfani da kudin yadda ya dace.”

Bukatarsa mafi girma ita ce karin dala biliyan $16.8 daga Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Tarayya, wanda akasari an yi nufin sake gina kadarori da ababen more rayuwa, tare da ware dala biliyan $5 don share tarkace.

Newsom ya kuma nemi dala biliyan $9.9 daga Ma’aikatar Gidaje da Ci gaban Birane don tallafin kudi ga wadanda gobarar ta shafa, masu gidaje, ‘yan kasuwa da masu haya, da kuma dala biliyan $5.29 daga Hukumar Kula da Kananan ‘Yan Kasuwanci don taimakawa masu gidaje da rance ga ‘yan kasuwa.

Newsom ya godewa shugaba Donald Trump game da taimakon gaggawa na kwashe tarkace. Sai dai wasikar ba ta ambaci barazanar da gwamnatin Trump ta yi a baya bayan nan ba cewa taimakon da gwamnati tarayya ke yi na iya zowa da tsauraran sharudda.

“Muna godiya sosai,” in ji Newsom.

Shugaba Trump ya kasance mai sukar Newsom da manufofin ruwa na Califaronia. Ric Grenell, abokin Trump da ke aiki a matsayin wakilinsa na ayyuka na musamman, ya fada a ranar Juma’a cewa, “Za’a gindaya sharudda” ga duk wani tallafin tarayya ga jihar.”

Ya ce daya daga cikin sharadodin da ake magana a kai shi ne na hana kudade ga hukumar kula da gabar tekun California, wacce ke kula da raya gabar teku da kuma hana jama’a zuwa bakin teku.

Trump ya soki hukumar a matsayin mai wuce gona da iri a matakanta, tsarin aikinta da kuma kawo cikas ga kokarin sake ginawa kan lokaci.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG