Wannan kiraye-kirayen sun biyo bayan wasu sabbin hare-hare ne da kisan mutane da ke aukuwa a wasu sassan jihohin.
A karshen makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kashe wasu matafiya bayan da motarsu ta lalace a kauyen Yalwata da ke kan iyakar jihohin Benue da Nasarawa.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Benue Alhaji Ubbi Haruna, ya tabbatar da cewa mutane 10 ne aka kashe ciki har da maza da mata da kananan yara.
Ya kuma kara da cewa akwai jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda a yankin amma har aka kashe mutanen babu wanda ya kai musu dauki.
Shi ma shugaban kungiyar matasan al'umar Tiv a jihar Nasarawa, Peter Ahemba, ya ce su ma an kai wa al’ummarsu hari a karshen makon jiya.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su samar da hanyar sasantawa don wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umomin yankunan.
Domin karin saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum