Cibiyar dake aikin tiyata wa masu lallrar yoyon fitsari dake asibtin Jankwano a Jos ta gudanar da bikin sallamar wadanda aka yiwa aiki suka kuma warke.
Ana gudanar da bikin ne kowace shekara yayinda ake tattaro duk matan da suka kamu da cutar da aka yiwa aiki suka kuma warke dominkarfafasu da fadakar da duk wacce ta kamu da cutar da cewa cuta ce dake warkewa kuma ana gudanar da aikin kyauta ne.
Wasu matan da suka kamu da cutar har na tsawon shekaru biyu zuwa talatin sun bayyana godiyarsu da irin taimakon da asibitin ya basu yayinda 'yanuwansu suka yi watsi dasu.
Matan ba'a barsu haka ba. Wasunsu sun koyi sana'o'i daban daban domin samun abun dogaro ga kai.
Likitan dake kula da cibiyar Sunday Lengman ya ce cibiyar ita ce daya tilo dake tara mata masu lallurar a duk fadin duniya. Ya ce kawo yanzu cibiyar ta yiwa mata fiye da 10,400 tiyata. Ya kira hukumomi su taimakawa cibiyar saboda bayan an yi masu tiyata kyauta yakamata a basu taimakon jari su kyautata rayuwarsu.
Daraktan dake aikin mishan a asibitin wanda cibiyar ke karkashin kulawarsa Tom Jethron ya yaba ne da gudummawar kudade da wasu kungiyoyin kasashen waje ke bayarwa wajen ci gaban cibiyar domin taimakon matan dake yoyon fitsari. Tom Jethron ya jaddada cewa kaunar Yesu Almasihu ta sa suke bada taimakon.
Wasu matan sun samu kekunan dinki da wasu kudade domin inganta rayuwarsu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum