Hukumar kiyaye haduran ababen hawa, FRSC, a jihar Filato ta ce za ta ci gaba da aikinta ta tabbatar cewa duk wani mai tukin abun hawa akan titunan Najeriya ya bi dokokin kasa.
Kwamandar hukumar ta jihar Filato Patricia Emordi ta bayyana hakan bayan wani zanga zangar da masu tuka kekenapep suka yi a Jos, babban birnin jihar. Zanga zangar ta kai ga lalata motocin hukmar da wasu motocin jama'a kana jami'an hukumar shida suka samu raunuka.
A cewar Patricia Emordi ta yi mamakin yadda matukan kekenapep din suka afkawa wani ofishinsu dake kan Ring Road. Ta ce an lalata masu motoci kimanin goma sha biyu da tagogin ofishinsu da takardun aikinsu. Injita dalili kenan hukumar ta ce dole ne su nemi lasisin tuka kekunansu kamar yadda masu motoci su keyi. Ta dalilin haka ne hukumar za ta sani ko shekarun wasunsu sun kai su tuka keken. Kudin lasisi na shekara uku ya dara Nera dubu shida kadan. Ta kira matukan su bi dokoki su kuma daina shaye-shaye.
Amma su masu tuka kekenapep sun koka ne akan kudi Nera dubu biyar da dari takwas da ma'aikatar sufurin jihar ta bukaci kowanensu ya biya domin a yi masu horaswa ta musamman tare da tattancesu.
Wasu matukan sun fusata ne da matakin da gwamnati ta dauka kan biyan kudin. Sun ce basu amince da biyan kudin ba sai gwamnati ta soke.
Biyo bayan zanga zangar, gwamnatin jihar ta dakatar da yin aikin sufuri da kekenapep din a birnin Jos da Bukuru a kokarin maido da doka da oda.
Yanzu dai talakawa da suka dogara ga kekenapep sun shiga wani halin lahaula wala kawati. Matuka keken ta nan suke samun cin abinci da ciyar da iyalansu. An kira gwamnati ta sake duba lamarin ta ji tausayin talakawa.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum