Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Akan 'Karin Haraji Tsakanin Amurka da China


Amurka ta fada a jiya Lahadi cewa tana sa ran China za ta maida martani wurin kara haraji a kan kayyakin da Amurka ke aikawa China, biyo bayan karin haraji da shugaba Donald Trump ya yi a kan kayayyakin China da za a shigo dasu nan Amurka.

Babban mai bada sahawara a kan tattalin arziki a fadar White House Larry Kudlow, ya fadawa shirin labaran Fox News na jiya Lahadi cewa bangarorin biyu sun sha wahalar wannan rikicin ciniki tsakanin Amurka da China, kasashe mafin karfin tattalin arziki a duniya.

A Amurka, ya ce babbar matsalar wannan rikicin cinikin zai fi tasiri ne a kan manoma masu sayar da waken Soya da Masara da Alkama. Amma ya ce gwamnatin Trump ta taba taimaka musu da dala biliyan 12 na tallafin haraji a baya a kan hasarar da suka yi wurin aikewa da kayansu kuma zamau sake taimaka musu idan yin haka ya taso.

Trump a ranar Juma’a ya yi karin fiye da kashi dari na haraji a kan dala biliyan 200 a kan kayyakin China, lamarin da ya cira harajin daga kashi 10 zuwa 25 cikin dari, ya yin da yake kokarin kara harajin dala biliyan 300 a kan wasu kayyakin China, sai dai Kudlow yace zai dauki wasu ‘yan watanni kafin a fara jin tasirin harajin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG