Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Jirgin Sama Ya Yi Sanadiyar Rayuka a Rasha


Jirgin sama ya kama da wuta a Rasha
Jirgin sama ya kama da wuta a Rasha

An kashe akalla mutane 40 a wani hatsarin jirgin saman daukar fasinja samfurin Sukhoi Superjet-100 da ya kama da wuta ya yin da yake sauka a wani filin saukar jirage na birnin Moscow a jiya Lahadi.

A cewar kafafen yada labaran Rasha, wani kamfanin sufurin jiragen sama a Rasha Aeroflot keda jirgin kuma yana dauke da fasinjoji 73 da ma’aikatan jirgin guda biyar. Wasu matasa biyu da daya a cikin ma’aikatan jirgin suna cikin wadanda suka mutu, inji kwamitin binciken Rasha.

Jirgin ya bar filin saukar jiragen saman Moscow da karfe shida na yamma agogon kasar zuwa birnin Murmansk dake arewacin kasar. Bayan wani lokaci kalilan da tashin jirgin sai matukan jirgin suka sanar an samun tangardar na’ura don haka akwai bukatar saukar gaggawa.

A yunkurin saukar ne sai injin jirgin ya kama da wuta ya yin da jirgin ya sauka a cewar kafafen yada labarai.

Kwamitin binciken Rasha yace ya bude bincike ko akwai wani aikata ba daidai ba a wannan hatsari. Koda yake ya zuwa yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG