Ghana ita ce ‘kasa ta biyu a nahiyar Afirka da ta sami wannan rigakafin, wanda ake sa ran za ta rage yawan cutukan da sauro yake yadawa. Amma kuma masana na cewa sauran matakan da ake dauka na kare kai daga cutar Maleriya suma sun zama dole.
Ya dauki sama da shekaru talatin da kuma kudi kusan dalar Amurka biliyan ‘daya kafin a samar da allurar rigakafin Maleriya, wadda aka kaddamar da ita a kasar Ghana.
Allurar rigakafin da aka fi sani da RTS-S, tana rage yawan cutukan da sauro ke yadawa ga kananan yara da kusan kashi 40 cikin 100.
Kasar Ghana da Kenya da kuma Malawi sune kasashen da aka kaddamar da shirin gwajin allurar rigakafin, wanda aka fara tun makon da ya gabata a Malawi. Cikin shekaru hudu masu zuwa ana sa ran yiwa yara miliyan ‘daya allurar rigakafin.
Birnin Cape Coast na daya daga cikin yankuna uku a Ghana da aikin ke aunawa dake fama da yawan zazzabin Maleriya.
Richard Mihijo na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya ce ana bukatar rigakafin ne domin ana samun koma baya a ‘yan shekarun nan.
Ya ce “wannan wani abu ne da muke kallonsa a matsayin ci gaba a fannin lafiya, saboda idan aka duba ya zuwa yanzu abubuwan da muka yi amfani da su domin yakar wannan cuta, mun yi imanin wannan saon rigakafin zai taimaka sosai a yakin da ake da cutar Maleriya.”
Hukumar WHO ta ce mutane miliyan 219 ne zazzabin cizon sauro ya kama a shekarar 2017, kuma ta kashe mutane dubu 435.
Facebook Forum