Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Venezuele:Juan Guaido Ya Nemi Taimakon Soji A Kawar Da Gwamnatin Maduro


'Yan adawa sun yi fito mu gama da jami'an tsaro a Caracas
'Yan adawa sun yi fito mu gama da jami'an tsaro a Caracas

Gwamnatin ‘yan gurguzu ta Venezuela ta ce ana yunkurin juyin mulki a Caracas, yayinda da shugaban ‘yan adawa da Amurka ke dauka a matsayin shugaban wucin gadi Juan Guaido, ke cewa “babu ja da baya” a yunkurinsa na kawar da shugaban kasa Nicolas Maduro.

Dubban masu zanga-zanga ne suka fita kan tituna a babban birnin kasar, sai dai sojoji masu goyon bayan Maduro sun tarwatsa su da harbin bindiga da kuma watsa musu ruwan zafi.

Wani hoton bidiyo da aka nuna ta gidan talabijin ya nuna yadda wata babbar motar sojoji ke bi ta kan masu zanga-zangar, wadanda ke jifansu da duwatsu. Gwamnati ta ce harbin bindiga ya samu daya daga cikin sojojinta.

A nan birnin Washington kuma, shugaban kasa Donald Trump ya fadi ta shafin Twitter cewa, yana lura da dukkan abin da ke faruwa, ya ‘kara da cewa “Amurka tana tare da mutanen Venezuela da kuma ‘yancinsu.”

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG