Firaministan jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya sauka a Abuja Najeriya don jiran yanda za ta kaya a matakan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afurka ta Yamma ECOWAS ta dauka na ba da wa’adin maida mulki hannun farar hula daga sojojin da su ka kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum.
Ouhoumoudou Mahamadou na wajen taro a kasar Italiya ne a ka samu labarin yin juyin mulkin don haka ya biya ta Istanbul a kasar Turkiyya kafin sauka a Abuja don ba hanyar shiga Nijar.
Babban mai ba da shawara ga firaministan Dr. Manzo Abubakar ya ce su na mara baya ga matakan ECOWAS da fatar samun sulhu maimakon kai wa ga fada tsakanin dakarun ECOWAS da sojojin da su ka kifar da gwamnatin.
Dr. Abubakar ya kara da cewa ba sa zargin Faransa ko Rasha da hannu a juyin mulkin da su ke ganin radin kan sojojin ne kawai don son zuciya su ka aiyana juyin mulkin.
Mai ba da shawarar ya ce sojojin gyauron wadanda su ka yi juyin mulki ne tun zamanin marigayi shugaba Ba’are Mainasara haka nan su ka sake maimaitawa kan marigayi Tandja Mammadou.
A shawarar Dr. Manzo Abubakar sojojin su gaggauta mika mulkin don hakan ne zai iya sa a yi mu su ahuwa in kuma sun ki ji ba sa ki gani ba.
A hangen Manzo saura kiris su nufi birnin Niamey don karisa wa’adin mulkin su na gwamnatin Bazoum.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna