Ta bakin mai tallafawa shugaban Najeriya ta fuskar labaru, Mallam Garba Shehu, ya baiwa gwamnonin shawarar su ware kashi 45 cikin 100 don biyan albashin.
Sai dai gwamnatin tarayyar tace wasu jihohin sun noke ko daukar wasu matakai da ba zasu shawo kan kalubalen da ake fuskanta ba. Garba Shehu, yace akwai jihar da ake binta bashin watanni 20, abin takaici shine wasu jihohin basu mayar da hankali wajen biyan albashi ba bayan da suka sami wannan kudi.
Rashin biyan albashi na kawo barazana ga kyakkyawar manufa da shugaba Mohammadu Buhari yake da ita akan ma’aikatan Najeriya - inji Mallam Garba Shehu.
Tuni dai masana ke shawartar gwamnatin tarayyar ta dage wajen bullo da hanyar yaki da talauci da hanyoyin samun kudin shiga ga aljihun talakawa ta hanyar kafa kamfanoni da hakko ma’adanai, wanda hakan zai taimaka wajen tururuwar neman aikin gwamnati.
Masanin harkar Man Fetur Injiniya Felani Mohammad, yace zai yi kyau idan ‘yan Majalisa su kayi bitar kudurin dokar albarkatun man fetur ya amfani dukkan sassan Najeriya, ba wai ya fi mayar da hankali ga Niger Delta ba kadai.
Dogaro ga man fetur kacokan ya janyowa Najeriya afkawar karayar arziki sakamakon faduwar farashin gangar man wanda ya tilastawa kasar neman karin hanyoyin kudaden shiga.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.