Da yake magana a taron shugaban Katolika na Abuja kuma tsohon shugaban kungiyar Kristoci na Najeriya CAN, Bishop John Onaiyekan, yace abin da ke kawo matsala a Najeriya shine mutum ya dauka addinin wani shine matsalarsa ko matsala ne a gareshi. Ya ci gaba da cewa ya zama wajibi mu zauna tare cikin fahimtar juna a Najeriya, don Allah da ake bautawa ‘daya ne.
Taron dai ya horas da matasa 100 daga jihohin Arewa 19 don su koma gida su yada akidar zaman lafiya, don kawo karshen fitinar nan irin ta kudancin Kaduna da karfawa jami’an tsaro gwiwa don kammalawa da burbudin Boko Haram da kawo karshen duk wani zaman doya da manja.
Onaiyekan, ya yabawa shugaban kungiyar Kristoci Rev Samuel Oyekulle, da yayi umarnn yiwa mukaddashin shugaba Buhari, Yemi Osinbajo da Najeriya addu’ar nasara har zuwa dawowar shugaban. Inda ya ‘kara da cewa wannan abin farin ciki ne an samu hadin kai kan wannan addua tsakanin Musulmai da Krista.
Shima shararren mai tattaki daga Legas zuwa Abuja bayan zaben 2015 don marawa shugaba Buhari baya, Sulaiman Hashim, ya nuna muhimmancin fatan alheri da hadin kan Najeriya ta hanyar addu’a.
Domin sauraron cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya danna ‘kasa.
Facebook Forum