Babban kwamandan hukumar kare hadurra a Najeriya, FRSC, Boboyemi Oyeyemi, ya ce kashi 90 cikin 100 na manyan motocin kasar sun tsufa da shekaru 20.
Oyeyemi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da shugaban hukumar hadahadar kasuwanci ta kan teku, kan sabbin wuraren dakatarwar manyan motoci da ake shirin kafawa a kasar.
Kwamandan ya kara da cewa samar da hanyar layin dogo shi ne kadai zai iya magance matsalar da ake fuskanta wajen isar da kayayyaki zuwa inda ake so su kai ba tare da wata matsala ba.
Ya bayyana cewa manya ko dogayen motoci za su iya taka rawa ne kadai wajen isar da kayayyakin zuwa tashoshin jiragen kasar domin a yi safararsu zuwa wurare masu nisa.
Wasu daga cikin shugabannin kungiyar direbobin manyan motoci sun yi na’am da wannan tsari sai dai sun ce akwai alamun gwamnati ta yi zari wajen aiwatar da wannan shiri idan aka yi la’akkari da irin makudan kudaden da ake so a kashe.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin jin karin bayani:
Facebook Forum