Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jam’iyyar PDP Ya Tare a Ofishinsa


Shugaban Jam'iyyar PDP Ali Modu Sheriff Da Magoya Bayansa
Shugaban Jam'iyyar PDP Ali Modu Sheriff Da Magoya Bayansa

Shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ali Modu Sheriff ya shiga ofis a hedikwatar jam’iyyar ta Wadata Plaza dake Abuja.

Sheriff wanda ke samun adawa daga bangaren jam’iyyar na Ahmed Makarfi, inda har wasu su kayi ‘yar zanga-zanga, yace yana da cikakken goyon baya ‘yan jam’iyyar ciki har da wasu gwamnoni da bai ambaci sunansu ba.

Tuni dai wasu magoya bayan Shariff daga jahar Imo suka kawo masa ziyarar mubayi’a da rere wakokin mara baya. An kammala sabon fenti a ofishin inda aka ga tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara kan siyasa Ahmed Gulak, na shiga da fita.

Sheriff ya nuna kwarin gwiwar samun nasara ‘daukaka ‘karan da kwamitin rikon jam’iyyar ya shigar kotun koli. Inda yace in har za a yi abu akan gaskiya to tabbas bashi da damuwa, kuma ba shugabancin ne ya dameshi ba, abin da ya dame shi shine jam’iyyar ta koma hannun mutanen Najeriya, maimakon wasu mutane kalilan su yi kaka gida.

Wasu matasan jam’iyyar dake neman gane alkiblar da ta fi karfi don su bi, suma sun halarci taron mara bayan. Tsohon ‘karamin Ministan Kudi Dakta Yarima Lawan Ingama, na kan gaba cikin masu ganin ya dace duk ‘yan jam’iyyar su hada kai da Sheriff, don raya adawa a Najeriya.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG