A Najeriya Majalisar Dattawa ta amince da daidaita mataki tsakanin masu digiri daga Jami'oi da masu takardar babbar difloma wacce aka fi sani da HND a turance.
Majalisar Wakilan Najeriya na shirin yin dokar da za ta soke shirin yi wa kasa hidima, NYSC bisa dalilin tabarbarewar Tsaro a kasar.
Dokar halitta tabar wiwi dake jiran a bude mata dandalin sauraren ba'asin jama'a ta hada da wasu sharuda kamar yadda Madam Mirian Onuoha, yar Majalisar Wakilai daga Jihar Imo wadda ta samar da dokar ta bayyana.
Takaddama ta kunno kai tsakanin kungiyar kwadago da kungiyar gwamnonin Najeriya kan cire tallafin Man fetur.
Majalisar Dattawan Najeriya ta na duba yiwuwar yi wa dokar rigakafin ta'addanci ta shekara 2013 kwaskwarima inda za a hana biya da karbar kudin fansa.
Hukumar Shige da Fice ta ce ta kafa takunkumi da bayar da faspo ga masu bukata a dukkanin Ofisoshinta da ke kasar har sai ranar 1 ga watan 6 Yuni.
Shugaba Mohammadu Buhari ya aika wa Majalisar dokokin Najeriya wata takardar neman izinin ya sake karbo bashin dalar Amurka biliyan 6.18 daga kasashen waje da manyan cibiyoyin hada hadar kudade na duniya.
Kungiyar mata ‘yan Jarida ta Najeriya NAWOJ, ta shirya wani taron addu'o'i don rokon Allah ya kawo karshen ayyukan ta'addanci da rashin tsaro da ke addabar tattali arziki da kuma zamantakewar al'ummar kasar.
Komitin Kula da Harkokin Kudi na Majalisar Dattawa a karkashin Jagorancin Sanata Solomon Adeola ya ce ya gano cewa, a cikin shekaru 5, Ma'aikatu da Hukumomin Gwamnati sun yi sama da fadi da kudade har Naira Triliyan 3 wadanda ba a sa su a cikin lalitar Gwamnati ba.
A karon farko bayan sun kwashi kwanaki 100 da kama aiki, shugabanin hukumomin tsaro a Najeriya sun kwashi kusan sa'o'i biyar suna ganawa cikin sirri da daukacin 'yan Majalisar Dattawan kasar kan yadda za a gano bakin zaren da zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da kasar ke ta fama da shi.
Gamaiyar yan adawa ta PDP a karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye Enyinanya Abaribe sun baiyana damuwarsu akan yadda Jamiyar APC mai mulki a karkashin shugaba Mohammadu Buhari ta kasa kawo karshen rashin tsaro a kasa, wanda shi ne muhimmin dalilin Kampe din su a shekara 2015.
Jam'iyyar Adawa ta PDP a Najeriya ta ce a shirye ta ke ta taimakawa gwamnatin APC a karkashin Shugaba Mohammadu Buhari domin magance ta6ar6arewar lamuran kasar a yanzu.
A yanzu mata 8 ake da su a Majalisar Dattawa, sannan 13 a Majalisar Wakilai - adadin da ke nufin kashi 4.4 a cikin 100 kacal ke Majalisar.
Matsalar garkuwa da mutane na kara zama babbar barazana ga mazauna wasu yankunan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Takkadama ta kunno kai tsakanin Gwamnan JIhar Edo, Godwin Obaseki da Ministar Kudi, Zainab Shamsunah Ahmed akan bayanan da Obaseki ya yi a wani faifan bidiyo da ya karade duniya cewa Gwamnati ba ta samu kudin da za ta ba Jihohi a karshen watan Maris ba.
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar da za ta taimaka wa hukumar kula da sha'anin dukiyoyin Gwamnati wato AMCON wajen ganin ta kwato wasu kudade da yawansu ya kai Naira Triliyan 5 a hannun wasu ‘yan Najeriya 20, wadanda suka karbi kudaden a matsayin bashi.
Kungiyar ma'aikatan kotunan shari'a a Najeriya,sun fari yajin aikin sai baba ta gani saboda matsa lamba ta samawa bangaren shari'a 'yancin cin gashin kai.
Al'umman Nijer mazauna Babban Birnin Tarrayyar Najeriya Abuja sun yi wata kwaryakwaryar liyafa na nuna farin cikin su da yadda aka samu sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali.
A Najeriya, Majalisar Dattawa ta aiwatar da dokar da za ta ba da damar kafa wata gidauniya wadda za ta ba manoma tallafi na taimakon gaggawa.
Domin Kari