Wanan dai ya biyo bayan taro ne na musamman da Jamiyyar ta yi a Abuja inda ta tattauna irin halin da Najeriya ta shiga a wannan lokaci da ke bukatar jinginar da banbancin Jamiyya da addini ko kuma siyasa.
A lokuta da dama Jamiyyar ta PDP ta sha sukar irin salon mulkin Jamiyyar APC, amma a wanan lokaci ta ce za ta jinginar da adawa da nufin taimakawa Jamiyya mai Mulki wajen magance ta6ar6arewar sha'anin tsaro da zaman dar dar da jama'an Najeriya su ke yi ko kuma suke fuskanta a sassan kasar.
A wajen taron, shugaban Jamiyyar PDP Uche Secondus ya ce lallai lokaci yayi da dole 'ya'yan Jamiyyar su baiwa gwamnatin APC goyon baya.
Bayan wadan nan jawabai na Uche Secondus, shi ma Sakataren Jamiyyar PDP Umar Ibrahim Tsauri ya kara jaddada manufinsu, inda yayi bayani cewa in an duba yanzu babu inda aka samu cigaba a dukan alkawuran da Jamiyyar APC ta yi a baya, Umar Tsauri yace adawar su tana nan kuma daban ta ke da irin adawar da APC ta ke yi,su ya ce ta su adawar a PDP ta gani ta fadi ce kuma ta taimakawa ceidan bukatan haka ta taso.
Amma kuma Shugaban rikon kwarya na Jamiyyar APC kuma gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce wannan al'amari dai tamkar tabarmar kunya ce wace ake nadewa da hauka,domin idan maye ya manta ai uwar 'ya ba za ta manta ba.
Mai Mala ya ce su PDP sun san irin halin da suka bar kasar a ciki. Ya ce sun kyale batun tsaro har ya gawurta, ya rarrabu kashi kashi, babu inda rashin tsaro bai ta6a ba a kasar, sai yanzu ne za su fito su ce za su taimaka wa gwamnati mai ci?
Karin bayani akan: PDP, APC, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Buni ya ce kamata ya yi PDP su nemi yafiya daga wajen yan Najeriya na mulkin kamakarya da suka yi a baya.
Mai Mala ya shawarta cewa a tasar ma dauka sojoji dayawa har da Yansanda saboda a kara yawan su don tsaro ya inganta.
A kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi ya sa Majalisar tsaro ta kasa ta amince da kafa wata hukuma da za ta sa ido kan hada hadar makami a kasar da nufin dakile motsi da su.
Saurari cikakken rahoton a sauti: