Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Ta Barke Tsakanin Gwamnan Edo Da Ministar Kudi A Najeriya


Ministar Kudi A Najeriya Zainab Ahmed.
Ministar Kudi A Najeriya Zainab Ahmed.

Takkadama ta kunno kai tsakanin Gwamnan JIhar Edo, Godwin Obaseki da Ministar Kudi, Zainab Shamsunah Ahmed akan bayanan da Obaseki ya yi a wani faifan bidiyo da ya karade duniya cewa Gwamnati ba ta samu kudin da za ta ba Jihohi a karshen watan Maris ba.

Ministar Kudi ta fito ta karyata shi, amma kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce aikinsa ne buga kudi, kuma lallai an buga kudi.

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi har Naira Biliya 60 a karshen watan Maris aka raba wa Jihohi.

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki
Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki

Amma Ministar Kudi Zainab Shamsunah Ahmed ta fito ta sifanta kalaman Gwamnan Obaseki a matsayin zancen da ba shi da tushe.

Sai dai Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce shi a fahimtarsa, Godwin Obaseki yana nufin an buga kudi an baiwa gwamnoni rance.

Karin bayani akan: Zainab Ahmed​, Babban Bankin Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Godwin Emefiele ya ce a shekara 2015 zuwa 2016 sun buga kudi sun baiwa gwamnoni rance, saboda ba zai yi wu Gwamnatin Tarayya ta zuba ido al'ummar Najeriya su shiga garari don rashin kudi ba a irin wannan lokaci da ake ciki.

Ya ce da gaske mun buga kudi amma rance muka baiwa gwamnoni.

Emefiele ya kara da cewa, yanzu tunda abin ya zama laifi a wurin gwamnonin da suka taimaka wa, za su tsaya da kafafun su sai sun biya kudaden da suka karba rance.

Kwararre a kimiyar tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati, ya ce buga Kudi yana da kaifi biyu, domin yana da alfanu kuma yana da illa.

Mikati ya ce, wannan kudi da Gwamnati ta raba wa jihohi ba za su biya ruwa akai ba shi ne alfanunsa, amma kuma in an ci gaba da buga kudi ana rabawa ba tare da wani aiki na musamman da za a yi saboda kudin su fita ba, hakan zai kara hauhawan farashin kayayyaki, kuma haka zai rage darajar kudin Najeriya.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya tsakanin gwamnonin Najeriya da Babban Bankin kasa, ko za a biya wadanan basussukan a cikin sauki kafin gwamnatin tarraiya ta kafa wani kotu na musamman da zai taimaka wa hukumar AMCON wajen kwato basussuka.

Saurari Rahoto Cikin Sauti Daga Medina Dauda:

Takaddama Ta Barke Tsakanin Gwamnan Edo Da Ministar Kudi A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00


XS
SM
MD
LG