Hakan na faruwa ne ganin cewa yanzu hukumar ta samu izinin sabunta faspo sama da 180,000 wadanda aka yi rajistar su ta yanar gizo.
Amma wasu yan kasa sun yi sukar yadda yin rajistar masu neman fasfo din yake daukan tsawon lokaci.
Shugaban Hukumar Shige da Fice ta kasa Muhammad Babandede ne ya bayyana daukan matakin dakatar da kar6ar fasfo din, domin warware wasu matsalolin da ake fuskanta.
Shi wanan fasfo din mai suna E-passport shi ne irin fasfo din zamani wanda za a hada shi da lambar zama dan kasa da kuma lambar ajiyan kudi a banki, kuma ya banbanta da wanda aka saba yi da takarda.
Abin da ya dauki hankali a wannan sabon fasfo din shi ne, guda daya ake yi, ba za a iya sauya shi ko kuma a yi angulu da kan zabo da shi ba.
Babandede ya ce yanzu yatsu duka guda goma ake amfani da su domin hana samun damar yin fasfo fiye da daya,.
Ganin cewa wadanan matakan kandagarki da aka yi a wanan fasfo din an yi su domin taimaka wa inganta tsaro a kasa, shi ne ya sa kwararre a kimiyar tsaro da diflomasiyar kasa da kasa Dokta Yahuza Ahmed Getso ya ce da ma jami'an ma'aikatar shige da fice din ne sukan aikata ba daidai ba, wurin karban makudan kudade a hannun masu neman samun fasfo fiye da daya.
Ganin cewa za a rika biyan kudin fasfo din ta yanar gizo ne, wasu sun yi suka kan yadda ake rajistar samun fasfo din, wani abu da Muhammad Babandede ya kara jaddada hanyoyin sauwaka samun fasfo din a lokacin da zai bude wasu kafofi a fadin kasar na kawo saukin aiki cikin lokaci kankani.
Daga yanzu har daya ga watan Yuni, Ofisoshin Shige da Fice ba za su kar6i sabbin aikace-aikace ba har sai an gama rarraba fasfo sama da dubu 180 din da ka samu izinin ba da su.
Saurari cikakken rahoton a sauti: