Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Zikirullahi Kunle Hassan ya sanar cewa tawagar hukumar zata tashi zuwa kasar Saudiyya a yau litinin yayin da jirgin farko zai tashi a ranar alhamis 9 ga wanan wata daga Maiduguri, Jihar Borno.
Kunle ya bayyani cewa, sai da suka tantance kamfanonin jiragen sosai kafin a amince da zabar wadanan kamfanoni uku da aka shiga yarjejeniyar da su.
Kunle ya kara da cewa, wadannan kamfanoni sun nuna kwarewa da bajinta a wannan lokaci na karancin man da ake amfani da shi a jiragen sama, saboda haka suna da yakinin kamfanonin za su iya aikin jigilar.
Shi ma Kwamishinan ayyuka na Hukumar Alhazan, Abdullahi Magaji Hardawa ya yi bayani cewa kudin kujera da alhazan Najeriya kasar za su biya domin yin hajjin na bana ya kai Naira Miliyan biyu da dubu dari biyar sabanin yadda aka biya a shekarun baya.
Shugaban Hukumar Alhazan Zikirullahi Kunle Hassan ya bukaci kamfanonin jiragen da su yi wa maniyyata kulawar da ta dace da su domin su samu saukin tsaida farali a lokacin aikin hajjin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: