Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Kafa Wani Kwamiti Da Zai Binciki Karin Kudin Da Kamfanonin Hadahada Suka Bullo Da Shi


Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)
Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya kafa wani kwamitin wucin gadi na mutum bakwai a karkashin mataimakin mai tsawatarwa Aliyu Sabi Abdullahi da zai binciki karin kudin fito da masu kamfanonin hadahadar shirye shiryen talabijin da ke aiki a kasar suka bullo da shi.

ABUJA, NIGERIA. - Hakan ya biyo bayan umurnin da majalisa ta baiwa kamfanonin da su gaggauta rage farashin su.

Wannan mataki ya biyo bayan wani kuduri mai dauke da korafi da sanata mai wakiltan Jihar Binuwai ta Kudu Abba Moro ya gabatar a zauren majalisar.

Abba Moro ya ce akwai kuka da ‘yan Najeriya ke yi a kai a kai a game da yawan karin kudin fito da kamfanonin nan ke yi babu kakkautawa.

Moro ya koka cewa ‘yan kasa na biyan kudi dayawa amma ba sa moran kudin saboda kalubalen da kasar ke fama da shi na wutar lantarki.

Mataimakin mai tsawatarwa a Majalisar Dattawan kuma shugaban kwamitin Aliyu Sabi Abdullahi ya ce kwamitin zai yi aiki bilhakki da gaskiya.

Kamfanonin Multichoice, DSTV da GOTV suna cikin wadanda kwamitin zai yi bincike akan yadda suke gudanar da ayyukan su a wannan kasar a cikin makonni hudu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Majalisar Dattawa Ta Kafa Wani Kwamiti Da Zai Binciki Karin Kudin Da Kamfanonin Hadahada Suka Bullo Da Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

XS
SM
MD
LG