Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisar Wakilai Sun Yi Kira Da A Rufe Majalisar Sabili Da Batun Rashin Tsaro


Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)
Majalisar wakilan Najeriya (Facebook/ Majalisar wakilai)

Batun rashin tsaro da ya kara ta'azzara a kasa ya sa an yi mahawara mai zafi a majalisar wakilai, yayinda wasu ‘yan majalisar suka nemi a rufe majalisar dokokin kasar.

ABUJA, NIGERIA - ‘Yan majalisar sun yi haka ne domin tilasta wa shugaba Mohammadu Buhari ya dauki kwararan matakai kan alhakin da ya rataya a wuyansa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

An yi musayar yawu da tada jijiyar wuya a majalisar wakilai kan kudurin gaggawa da dan majalisa mai wakiltan Birnin Gwari da Giwa ta Jihar Kaduna Shehu Balarabe ya kawo akan hari da aka kai kan jirgin kasa da ke sufuri tsakanin birnin tarayyya Abuja da Kaduna, da yawan kashe kashen Jama'a da ake ta yi a kasa babu ji babu gani, musamman a kananan hukumomin birnin Gwari da Giwa.

‘Yan majalisan sun yi suka da kakkausar murya da korafi kan mai ba shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro, Babagana Monguno inda suka nemi yayi murabus ko kuma a kore shi gaba daya domin ya gaza.

Daya cikin 'ya'yan majalisar wakilan Aminu Suleiman daga Jihar Kano ya koka da yadda kasar gaba daya ta kasance cikin mummunan rashin tsaro musamman ma rikicin da ke faruwa a yankin Arewa masa Yamma da ya ke kara kamari inda ya bada shawarar a rufe majalisar kasar baki daya har sai an samu mafita.

To sai dai sabon shugaban Jamiyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ce tsaron kasa hakki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa saboda haka a hada kai a yaki rashin tsaron.

Majalisar wakilan da mataimakin kakakin ta Idris Ahmed Wase ya jagoranta, ta ce dole ne gwamnati ta tashi tsaye wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyanta cikin gaggawa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

‘Yan Majalisar Wakilai Sun Yi Kira Da A Rufe Majalisar Game Da Batun Rashin Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG