Trump ya fadawa shugaban Cocin Katolikan a yayinda suka zauna a dakin karatun Paparoma na musamman cewa, “Wannan babbar karramawa ce.”
‘Yan sandan Burtaniya sun tsare wasu mutane uku sakamakon binciken da ke da alaka da harin Bom din da aka kai ranar Litinin din da ta gabata, a lokacin wani wasan raye-raye da kade-kade a Manchester.
Biyo bayan sandar da sanya takunkuman da Amurka tayi ya sa Iran shirin sanyawa wasu 'yan Amurka takunkumi.
Shugaba Trump ya koka akan cewa ba wanda aka taba nadawa ya bincike Hillary Clinton da tsahon shugaba Barack Obama.
Mayakan Kungiyar Taliban sun ce ba su da hannu a wannan mummunan harin da aka kai.
Mutane shidda ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bom na mota da aka kai a kasar Somaliya.
Shugaba Trump yayi ta kare kansa a wannan satin bayan da kafafen yada labarai suka bada rahoton cewa ya bada bayanan sirri na tsaro ga Lavrov da kuma Jakadan Rasha Sergei Kislyak.
'Yan majalisar Tarayyar Amurka na bukatar wasu rubuce rubuce daga tsohon shugaban hukumar FBI da aka kora, akan zargin matsin lambar da shugaba Trump yayi masa don yayi watsi da binciken Flynn.
Sojojin wanzar da zaman lafiya guda hudu ne 'yan bindiga suka kashe a kudu maso gabashin Afrika ta tsakiya.
A yau Laraba ne aka rantsarda Moon bayan da ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a kasar jiya talata.
Ana kyautata zaton batun Syria ne kan Gaba a ganawar da jami'an diplomasiyyar zasu yi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta sami rahoto mai ta da hankali na karuwar mace-macen mata da suka danganci rikici a Afghanistan da kashi 54, da kuma karuwar mace-macen kananan yara da kashi 17 a cikin watanni 4 na wannan shekarar ta 2017.
Kasashen Kenya da Habasha sun yi amfani da karfin soja wanda ya wuce kima akan fararen hular kasar Somalia a daidai lokacin da ake kokarin dakile hare-haren ‘yan kungiyar al-Shabab da ke kai kawo akan iyakar kasashen, a cewar wani rahoto da cibiyoyin agajin dake aiki a Somalia suka fitar.
An tsinci tsohon dan wasan kwallon kafar Amurka, Aaron Hernandez a mace a cikin dakinsa na gidan yari dake jihar Massachusetts a nan Amurka.
A yau Laraba an cigaba da aikin kwashe mutane a garuruwan Syria da aka yi wa kawanya, bayan da aka dakatar da aikin, biyo bayan wani harin bam da ya halaka akalla mutane 126.
Ta wayar Tarho ne shugaba Donald Trump ya gana da shugaba Xi Jinping, a cewar kafafen yada labaran China
Jami'an Kidaya aka auna a harin da a aka kai birnin Lahore a lokacin da suke cikin motarsu, a cewar hukumomin Pakistan.
Babu abinda ke nuna mutanen da aka kama a St. Petersburg na da alaka da harin ranar litinin, amma ana zargin su da sanya mutane cikin kungiyoyin 'yan ta'adda
Babu wanda ya dauki alhakin harin da aka kai a birnin Mogadishu wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai.
Wakilan gwamnatin Amurka zasu kai ziyara karo na farko kasar Afghanistan kwanan nan.
Domin Kari