Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Gana Da Shugaba Xi Jinping Akan Koriya ta Arewa


Ta wayar Tarho ne shugaba Donald Trump ya gana da shugaba Xi Jinping, a cewar kafafen yada labaran China

Kafafen yada labaran kasar China sun ce shugaba Xi Jinping ya fadawa shugaban Amurka Donald Trump cewa kamata yayi a warware rigimar da ake yi da Koriya ta arewa cikin lumana.

Rahotanni sun ce shugabannin biyu sun tattauna ne ta wayar tarho a yau Laraba, kusan mako daya bayan ganawar ido-da-ido da suka yi a taron kolin da suka yi a jihar Florida ta Amurka. Har yanzu dai fadar White House bata bada cikakken bayani kan tattaunawar da shugabannin biyu suka yi yau ta wayar tarho ba.

A jiya Talata, shugaba Trump yayi amfani da shafinsa na twitter don sake yin kira ga China akan ta taimaka wajen takawa Koriya ta arewa burki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG