A halin yanzu kuma, a yau ne Sakataren Harakokin Wajen Amurka Rex Tillerson yake karbar bakuncin takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov. Ana ganin ganawarsu zata ta’allaka ne kacokan akan sabanin ra’ayin dake tsakanin kasashensu biyu akan Syria.
Ana kuma sa ran cewa Lavrov zai gana da shugaba Donald Trump, a ziyarar farko da zai kai fadar White House tun bayanda aka zabi shi Trump din.
A cikin watan jiya ne Lavrov da Tillerson suka yi taro a Moscow kan cece-kuccen da ya barke a tsakanin Amurka da Rasha kan harin da Amurka ta kai kan wani filin jirgin saman Syria, bayanda jiragen Syria suka yi anfani da makamai masu guba akan fararen hulan da suka hada da kananan yara.
Facebook Forum