Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Gana Da Paparoma Francis a Vatican


Trump ya fadawa shugaban Cocin Katolikan a yayinda suka zauna a dakin karatun Paparoma na musamman cewa, “Wannan babbar karramawa ce.”

Shugaban Amurka Donald Trump da Paparoma Francis sun yi zaman tattaunawa ta tsawon minti 30 a birnin Vatican a yau Laraba, wanda ya jaddada muhimmancin ziyararar shugaban zuwa kasashen ketare ga addinan nan guda uku na Ibrahimiyya.

Shugaba Trump da Paparoma sun sha hannu da suka hadu da farko. Amma Paparoma dai ya dake, shi kuwa shugaba Trump sai dai yayi ta dan murmushi.

Bayan tattaunawar sirri da suka yi a fadar Paparoman, an kara yawan tawagar wakilan Amurka da suka shiga wurin ganwar na dan lokaci, ciki harda Uwargidan shugaban na Amurka, Melania Trump wacce ta sanya bakaken kaya da bakin mayafi, da Sakataren Harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da mai bada shawara kan harkokin tsaro Herbert Raymond McMaster, da kuma ‘yar Trump Ivanka tare da mijinta Jared Kushner, wadanda dukansu jami’ai ne dake bada shawara ga shugaban kasa.

Gaisuwar ta hada da ba bada kyututtuka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG