Kwamitin bincike a kasar Rasha ya ce ya kama mutane shidda ‘yan kasashen nahiyar Asiya ta tsakiya a birnin St. Petersburg bisa tuhumarsu da ake yi da bada tallafi ga ayyukan ta’addanci, kwanaki biyu bayan mummunan harin da aka kai a wata tashar jiragen kasa ta karkashin kasa a birnin.
Ana zargin mutanen da laifin sanya mutane daga yankin tsakiyar kasashen Asiya shiga kungiyar ISIS da wasu kungiyoyi na masu tsattsauran ra’ayi tun daga shekarar 2015.
Amma kwamitin ya fidda wata sanarwa mai cewa ba a sami wata hujja ba dake nuna mutanen da aka kama na da alaka da harin bom din da aka kai a birnin na St. Petersburg ba, wanda ya kashe mutane 14, mutane fiye da goma kuma suka jikkata.
Masu binciken kasar Rasha sun gano cewa Akbarzhon Jalilov dan shekaru ashirin da biyu da haihuwa, haifaffen Kyrgistan shine maharin da ya kai harin kunar bakin waken.
Facebook Forum