A makon jiya ne dai aka jiyo tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso a cikin wani sautin bidiyo yana cewa zasu bai wa gwamna mai jiran gado shawarar ya waiwayi batun yadda aka kirkiro da sabbin masarautu guda hudu a jihar da ma sigar da aka bi wajen tube rawanin sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido na biyu kimanin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai a jawabinsa na bikin ranar ma’aikata ranar Litinin, gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace sabbin masarautun da gwamnatinsa ta kirkiro zasu ci gaba da wanzuwa har bayan gwamnatinsa.
Sai dai al’umar jihar Kano sun bayyana abubuwan da suke gani ya kamata sabuwar gwamnatin da zata karbi ragamar mulki ta maida hankali akansu bayan rantsar da ita.
“Kwankwaso na maganar za a rushe, Ganduje na cewa ba za a rushe ba, mu al’umar jihar Kano ba wannan ne a gabanmu ba, ci gaban rayuwar al’uma shi ne a gabanmu, muna bukatar hanya, muna bukatar ruwa da lantarki,” a cewar wani mazaunin birnin Kano a yayin zantawa da Muryar Amurka.
Hakazalika, wani mazaunin karamar hukumar Nasarawa a birnin Kano cewa yayi, “mu babban burinmu shi ne gwamnati mai shigowa ta gina mana tituna, musamman titin bayan Airport daga Kings College zuwa Jaba a yankin karamar hukumar Nasarawa, wannan shi ne abin da muke bukata ba wai wadannan rigingimu ba, domin babu abin da zasu kawo mana illa ci baya.”
Amma a nasa bangaren, Comrade Yahaya Shu’aibu Ungogo, guda daga cikin masu sharhi kan al’amuran yau da kullum a Najeriya na cewa, “bisa kididdigar da aka bayar, akwai matasa da suke cikin harkokin shaye-shaye fiye da miliyan biyu a jihohin Kano da Jigawa, don haka da kirkiro masarautu da ruguza masarautu duk wasu abubuwa ne na siyasa. A saboda haka, ya kamata a maida hankali kan muhimman abubuwa.”
Shi kuwa Dr. Kabiru Sa’idu Sufi, malamin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano cewa yayi, “a nazarce za a iya cewa samun takun saka da cece-ku-ce a lokacin da gwamnati ke fita wata ke shiga ba sabon lamari ba ne, musamman idan aka samu bambancin jam’iyya, amma da zarar an karbi mulki za a shagala da manya kuma muhimman al’amura da suka shafi al’uma”
Abin jira a gani dai shi ne yadda zata kasance bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika madafun iko ga sabon gwamnan jihar Abba Kabiru Yusuf a ranar 29 ga wannan wata na Mayu.
Saurari rahoton Mahmud IbrahimKwari.