A yayin yakin neman zabensa, shugaba Tinubu mai jiran gado ya yi alkawarin kyautata rayuwar ‘yan Najeriya ta kowace fuska.
Watakila hakan ya sa ‘yan Najeriya suka fara tsokaci game da abin da suke sa ran fara gani daga gwamnatinsa.
“Muna so ya sauko da farashin canjin dala kuma ta wadatu domin mu rinka sayo kayayyaki cikin sauki daga waje. Sannan kuma a kawo tsarin da za a ba ‘yan kasuwa bashi mara ruwa, saboda mu musulmi ne ba ma karbar bashi da ruwa” a cewar wani karamin dan kasuwa a birnin Kano.
Hakazalika shi ma wani mazaunin garin cewa yayi, wannan gwamnati dai mun sa ido, kuma mun ce Allah yayi mana zabi ya kuma zaba mana. In har ya samu abokan aiki na gari, yadda ya yi wa Lagos aiki babu shakka muna sa ran ganin ya yi wa Najeriya hakan.
Wani matashi mazaunin birnin Kano ya ce suna sa ran za a samu sauyi ta bangaren tattalin arziki da kuma tsaro, domin suke damun arewacin Najeriya da Najeriya baki daya.
Ko da yake, tun a lokacin kamfe sabon shugaban na Najeriya ya tallata jaddawalin manufa da alkibilar gwamnatinsa, amma Sanata Masa’ud El-Jibril Doguwa tsohon wakili a majalisar dattawan Najeriya daga jihar Kano, na ganin akwai bukatar sabunta ji daga bakin ‘yan Najeriya kan yadda sabon shugaban zai bullo wa matsalolin kasar.
“Ya kamata su tara mutane daga bangarori dabam-daban, kamar Malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan boko da sauransu, don a sake duba menene bukatun mutane domin ayi abin da yace,” a cewar Doguwa.
Batun cire wa ko ci gaba da biyan kudaden da gwamnatin ke sanya wa a hada-hadar albarkatun mai a matsayin tallafi ga ‘yan kasa na cikin kalubalen da sabuwar gwamnatin zata tunkara, amma Alhaji Auwalu Abdullahi Rano shugaban gungun kamfanonin A.A RANO, kuma jigo a bangaren harkokin cinikayyar albarkatun mai a Najeriya na cewa, gwamnati na kokari wajen cika wa ‘yan Najeriya kudin mai domin rage farashinsa, amma wannan sabon shugaban ya ce zai duba lamarin kuma zai yi abin da ya kamata domin magance duk matsalar da ta dabaibaye harkokin cinikayyar albarkatun mai, kuma kungiyar zata bashi shawarar da ta kamata domin cimma nasara.
Bangaren masana’antu na da alaka ta kud-da-kud da batun albarkatun mai, kuma shi ne jigo ga sha’anin samar da aikin yi ga ‘yan kasa da kuma kudaden shiga ga gwamnati.
Ko da yake shugaba Tinubu ya yi alkawari na musamman ga wannan fanni, amma Alhaji Sani Hussaini Birnin Kudu, mamba a majalisar koli ta kungiyar masu masana’antu ta Najeriya, ya zayyana abubuwan da suke sa ran fara gani daga gwamnatin Tinubu.
“Muna so a sanya kwarya a gurbinta, wato a nada wadanda suka dace a ma’aikatu da hukumomin da ke kula da bangaren harkokin masana’antu kuma muna bukatar a saukaka canjin dala da samar da yanayin da ya dace ga masana’antu ta hanyar samar da wutar lantarki da kuma rage farashin man dizal”
Sai dai a nasa bangaren, Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, da ke koyar da kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano, na ganin tilas ne gwamnatin Tinubu ta fara da wasu abubuwa da jama’a zasu gamsu da cewa babu shakka sauyi ya zo.
“Gwamanti ta dauki matakan rage tsadar rayuwa, da magance matsalolin tsaro, da kirkiro da hanyoyin guraben aiki a gwamnati da cibiyoyi masu zaman kansu cikin sauri da sauki, idan tayi haka jama’a zasu yarda ta zo da gashi”
Abin jira a gani dai shi ne yadda gwamnatin ta shugaba Bola Ahmed Tinubu zata sarrafa shawarwari daga masana da sauran ‘yan kishin kasa wajen warware dinbin kalubale da Najeriya da kuma ‘yan Najeriyar ke fama dasu nan da shekaru 4 masu zuwa, lokacin da wa’adinta zai cika.
Saurari rahoton a sauti: