Yau Laraba a karo na biyu cikin tsauraran matakan tsaro, aka gurfanar da wasu mutane uku a gaban kotun majistire ta Kano, cikinsu har da Abdulmalik Tanko, wato mutumin da ake zargi da garkuwa tare da kashe dalibar makarantar sa, ‘yar shekaru 5 a duniya, Hanifa Abubakar.