Masu noman albasa da sarrafa ta da kuma kasuwancin ta daga kasashen nahiyar Afrika ta yamma da Afrika ta Tsakiya sun hallara a birnin Kano domin gudanar da taron yini uku wadda zai maida hankali kan lalubo hanyoyin magance kalubalen da suke fuskanta da kuma inganta hada-hadar cinikayyar Albasar a tsakanin kasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya.
Wakilai daga kasashen Ghana da Jamhuriyar Nijar da Gabon da Burkina Faso da Jamhuriyar Jamhuriyar Kamaru da Chadi da kuma Togo na daga cikin mahalarta taron
Alhaji Muhammadu Tasiu daga birnin Accra na kasar Ghana ya ce rashin daidaitaccen farashin albasa na daga cikin kalubalen da suke fuskanta wajen cinikayyar ta.
Kimanin ton miliyan biyar ne na albasa ake nomawa a duk shekara a nahiyar Afrika.
Dangane da haka ne Alhaji Tsalha Abubakar daga Jamhuriya Nijar ke cewa ya kamata mahukunta a kasahen Afrika su sassauta harajin da suke karba a hannun masu cinikayyar albasa baya ga tallafawa manomanta.
Taron dai na fatan tattaunawa tare da fito da matsaya akan wadannan dama sauran batutuwa, in ji Alhaji Aliyu Metasamu Isa.
Baya ga manoma da masarrafawa da kuma ‘yan kasuwar albasa, hukumomin aikin noma da Jami’an kwastam dana ma’aikatar ciniki da masana’antu na halaratar taron.