Dinbin jami’an tsaro suka kawo Abdulmalik Tanko cikin kotun majistiren Kano da ke gidan Murtala tare da sauran mutane biyu da ake tuhumar su tare.
Nan take ba tare da jinkiri ba, daraktar kula da kararraki ta ma’aikatar shari’a ta jihar Kano Barr. Aisha Mahmud ta sanar da kotun cewa, lauyoyin gwamnati da ta ke jagoranta a wannan shari’a sun kammala shirya cajin tuhuma akan mutanen uku, kuma suna muradin mayar da wannan shari’a zuwa babbar kotun jihar Kano domin fara shari’ar gadan gadan.
Kai tsaye dai alkalin kotun ya amince da wannan bukata.
Bayan fitowa daga zauren kotun, Barista Aisha ta bayyana cewa, bisa ga binciken ‘yan sanda sun yi nazari sun ga kotun majistare ba ta da hurumin saurarar shari’ar, saboda haka sai suka kai shari’ar gaban babbar kotun jihar wacce zata bada ranar da za a gurfanar da mutanen a gabanta.
Baristar ta kara da cewa ana tuhumar mutanen 2 da laifuffuka biyar, ciki har da hadin baki. Fatima matar Abdulmalik, ana cajin ta da laifin taimakawa wajen wannan mummunar aika aika saboda ita ta rubuta wasikar da aka turawa iyayen Hanifa, sai kuma Hashimu wanda shi ma ke da hannu a lamarin ake tuhumar shi da Fatima da laifin yunkurin sace hanifa. Shi kuma Abdulmalik aka caje shi da laifin yin garkuda da kuma kisa.
A wani labarin kuma, hukumar NAPTIP mai yaki da safara da fataucin bil’adama ta Najeriya, hadin gwiwa da jami’an tsaro na Jamhuriyar Nijar sun kubutar da wasu matasa su 61, yayin da masu safarar mutane ke yunkurin kai su kasar Libya.
Mr. Yohana Haruna, shi ne jagoran ayarin jamai’an da ke sintiri na musamman a ofishin shiyyar Kano na hukumar ta NAPTIP, ya ce cikin mutanen 61 sun gano mutun 2 da ake zargi da safarar mutanen da aka kama, kuma idan bincike ya tabbatar da hakan to za a gurfanar da su gaban kotu.
Mr. Haruna ya kuma ce mutanen da galibin su matasa ne, daga jihohin Lagos, Osun, Ondo, Oyo, Kwara, Edo, Delta, Niger, Gombe, Akwai-Ibom, Kogi, Cross River, Ebonyi da kuma Imo suka fito.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.