A karon farko Ministan harkokin Sufuri Najeriya Rotimi Ameachi ya kai ziyarar duba aikin shimfida layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna wadda gwamnatin tarayya ta fara.
Ziyarar na zuwa ne a dai-dai lokacin da wasu daga cikin mutanen da aikin ya shafi gonakinsu ke korafin rashin adalci wajen biyan su diyya.
Kimanin watanni 7 da suka shude ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin da wani kamfanin kasar China ke yi akan biliyoyin daloli, bisa alkawarin kammalawa a shekara ta 2023.
A cewar Ameachi, dalilin zuwan sa Kano domin sanin mizanin aikin dama ganin yadda aka fara aiwatar da shi, yana mai cewa ba za mu yi yabo ko kushe wa ba, an dai shimfida ginshikin aikin, kuma ko za’a yaba ko a kushe sai an je gaba.
Karamar tashar dauka da sauke fasinjoji da aka tsara yi a garin Yankin Madobi kafin shiga birnin Kano na cikin wuraren da ministan ya ziyarta.
Ko da yake, dukkanin al’umomin da wannan aiki ya keta garuruwa ko gonakinsu suna maraba da wannan ci gaba da gwamnatin tarayya ta kawo amma suna korafi kan batun biyan su diyya.
Malam Sulaiman Idris Dashi a yankin karamar hukumar Kiru ya ce “wannan aiki na layin dogo ya bi ta kan gonakinsa guda uku, da na kannena gaba daya, amma naira dubu 250 aka ba shi diyya, ko da yake, daga bisani an kara masa naira dubu 50. kawai dai ana zuwa a dau hotonka a gonarka a ba ka dubu 50.”
Shi kuwa magidanci Muhammadu Tasiu Yako Madobi, cewa ya yi, “darajar gonata za ta kai miliyan daya, kuma mutane da yawa ma ba a ba su komai ba, saboda ba su da inshora.”
Dangane da wannan batu Minista Ameachi na cewa, “kafin mu fara sai da muka biya kowa diyya domin shi ne matakin farko na aikin.”
Alhaji Sagir Sulaiman da ke zaman manajan shiyyar arewa maso yamma cin Najeriya, na kamfanin dake kula da kadarorin hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya ya ce an ba kowa hakkinsa
“Mun yi kokarin biyan duk wani da muka sani yana da hakkin a wajen, yawanchin su ba gine gine bane aikin gonakine.” Sulaiman ya ce.
Hakan dai na alamta bukatar gwamnatin tarayyar ta sake bitar wannan lamari domin tabbatar da adalci da jinkai ga alumma.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: