Sa'o'i kadan da sakin faya-fayan bidiyo har biyu na mutanen da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna, a Litinin din nan da rana, 'yan-bindigan sun sake sakin wasu mutane uku cikin wadanda aka nuna su na dukan su cikin faifan bidiyon jiya Lahadi.
Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald da ya shiga tsakanin 'yan-bindiga da iyalan mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna, Malam Tukur Mamu da kuma 'yan-uwan wadanda aka sacen sun tabbatar da sahihancin faifan bidiyon da ke yawo a yanar gizo inda 'yan-bindiga ke dukan mutanen.
Al'umar karamar hukumar Birnin Gwari sun ce sabuwar kungiyar nan mai kama da ta Boko Haram da ake kira Ansaru na kara karfi a wasu sassan karamar hukumar kuma har shugabaanni ta sun hana mutanen yankin shiga harkokin zabe.
Duk da artabun da aka yi tsakanin 'yan-bindiga da wasu jami'an tsaron da su ka sami hadin kan 'yan- sintiri a kudancin karamar hukumar Birnin Gwari a jahar Kaduna, 'yan-bindigan su sake kai wani hari inda su ka kashe wasu manoma a yankin Ganin-Gari na karamar hukumar.
Muryar Amurka ta yi hira da daya daga cikin mutane bakwai da 'yan bindiga su ka saki na baya bayan nan, daga cikin fasinjojin jirgin kasar da aka yi garkuwa da su sama da kwanaki dari da su ka shige.
Bayanai sun yi nuni da cewa har yanzu akwai sauran mutum 44 a hannun 'yan bindigar dajin.
‘Yan bindigar da su ka kai hari kan jirgin kasar da ke kan hanyar Kaduna-Abuja sun sako karin mutane bakwai bayan sama da kwanaki 100 da garkuwa da su.
A daidai lokachin da mutanen da 'yan-bindiga suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ke cika kwanaki 100 a Laraba mai zuwa, 'yan uwa da iyalan wadanda aka sacen sun ce su na cikin zaman zullumi.
Ganin yadda ake jingina hare-haren 'yan-bindiga akan makiyaya a Najeriya, ya sa wasu manyan kasa kafa wata sabuwar kungiyar kare harkokin makiyayan da ake kamawa ba tare da laifin komai ba.
Litinin din nan ne ake cika kwanaki 80 da kai harin da 'yan-bindiga su ka yi a jirgin kasan Abuja-Kaduna, inda su ka sace mutane da dama kuma su ka kashe wasu.
Duk da bayanin gwamnatin jihar Kaduna game da taimakon da al'umamr garin Dogon noma su ka ce jirgin sama ya yiwa 'yan bindigar da su ka kai musu hari wanda gwamnatin ta musanta, shugaban kungiyar al'umamr Adara ya ce su ba su gamsu da bayanan gwamnatin ba.
Al'ummar yankin Birnin Gwari sun ce tun da hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ta zama tarkon mutuwa to sun yanke shawarar kauracewa hanyar baki daya har sai mahukunta sun dauki mataki.
Kungiyoyi da al'umomi daban-daban na cigaba da Allah wadai da kisan da 'yan-bindiga su ka yiwa Harira mai dauke da juna biyu da 'ya'yan ta hudu a jahar Anambra.
A karshe dai 'yan-bindigan da su ka sace mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun bada wa'adin mako daya ga gwamnatin tarayya kan sako yaran wasu 'yan-bindigan da su ka ce idan ba haka ba, za su fara daukar mataki
Domin Kari