Gwamnatin jahar Kaduna ta ce lamarin tsaro a fadin Jahar ya kara ta'azzara masamman ma ta adadin mutanen da 'yan-bindiga su ka kashe da kuma wadanda aka sace cikin watanni ukun farkon wannan shekarar
A yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, kungiyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Kaduna ta ce ba za ta lamunci sabawa aikin jarida don kambama 'yan siyasa ba.
A yayin da al'umar Musulmi ke bukukuwan sallar idi a fadin duniya, 'yan'uwan mutanen da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun ce su na cikin kunci da damuwa sannan kuma sun tabbatar da cewa labarin da ake yadawa na sako Sadiq Ango Abdullahi ba gaske ne ba.
Gwamnatin jahar Kaduna ta jawo hankalin al'umma game da rahoton dasa abubuwa masu fashewa a wasu sassan jahar Kaduna lokacin bukukuwan sallar dake tafe.
Ganin yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula da rashin tsaro a wasu sassan jihar Kaduna da Najeriya baki daya ya sa kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN cewa lokaci ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi tsaye don magance matsalar tsaro a Najeriya.
Duk da gangarar karewar wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ce wajibi ne shugaban kasa ya ajiye mukamin shi saboda gazawar da ya yi na kare rayukan mutane da dukiyoyi.
Kwanaki sha biyar da kai harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, 'yan uwan mutanen da aka sace sun ce lokaci ya yi da gwamnati ya kamata ta nemawa wadanda aka kama mafita tunda 'yan bindiga sun ce da gwamnati za su yi Magana.
A daidai lokacin da al'umomi a wasu sassan Jihar Kaduna ke fama da hare-haren 'yan-bindiga da sace-sacen mutane don neman kudin fansa, wasu al'umma a yankin karamar hukumar Birnin Gwari sun ce akwai wasu mutane da ake kira 'yan-Ansaru dake yawan zuwa garuruwan su dauke da manyan makamai.
Har yanzu dai 'yan'uwan wadanda 'yan-bindigan suka tare a hanya na ci gaba da binchiken inda 'yan'uwansu su ke yayin da wadanda suka tsira ke jinya a asibitoci daban-daban.
Babban bankin Najeriya ya ce dalar masarar da aka kaddamar a Jihar Kaduna alama ce cewa gwamnatin tarayya ta inganta noma ta yadda za a iya fitar da masara zuwa kasashen waje.
Kwana biyu da kai harin da 'yan-bindiga su ka yi a wasu garuruwan karamar hukumar Kaura da ke kudancin Kaduna, gwamnatin jihar ta fitar da sunayen mutanen da aka kashe da kuma asarar dukiyar da aka yi.
Kungiyar Kiristan Najeriya, CAN, ta ce 'yan bindiga sun kashe mutane sama da ashirin sannan su ka kone gidaje da dama a wasu unguwanni uku a masarautar Kagoro da ke kudancin Kaduna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce kalaman Jagoran 'yan bindiga Bello Turji na neman sulhu alamu ne cewa addu'o'in al'umma na karbuwa wajen kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a fadin jihar baki daya.
Domin Kari