Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Saki Karin Fasinjojin Jirgin Kasa 3 Da Aka Sace


Fasinjoji uku da 'yan bindiga suka sake.
Fasinjoji uku da 'yan bindiga suka sake.

Sa'o'i kadan da sakin faya-fayan bidiyo har biyu na mutanen da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna, a Litinin din nan da rana, 'yan-bindigan sun sake sakin wasu mutane uku cikin wadanda aka nuna su na dukan su cikin faifan bidiyon jiya Lahadi.

A safiyar Litinin din nan ne dai 'yan-uwan mutanen da 'yan-bindigan su ka sace su ka yi zanga-zanga a Abuja da Kaduna domin nuna damuwa game da cigaba da rike 'yan-uwan su da 'yan-bindigan ke yi a daji. Ana cikin wannan zanga-zanga sai ga labarin sakin mutane uku daga ciki kamar yadda Malam Abdul-Azeez Attah da ke da 'yan-uwa biyu a hannun 'yan-bindigan ya tabbatar.

Attah ya ce sakin mutane ukun ya biyo bayan sulhu ne da tattaunawa tsakanin 'yan-bindigan da kuma iyalan wadanda aka sako amma babu hannun gwamnati a ciki. Ya ce mahaifiyar shi wadda ke hannun 'yan-bindigan ta tsufa sosai amma ita har yanzu ba a sake ta ba.

Barrista Hasan Lawal Usman na cikin mutane ukun da 'yan-bindigan su ka sako su jiya Litinin da rana kuma ya ce dalilin sakin faifan bidiyon da aka nuna ana ta dukan su a karshen mako shine yadda gwamnati ta ki bari 'yan-uwan su su shiga daji don karbo su.

Ya ce duk da shakar iskar 'yancin sakin shi, har yanzu ya na cikin damuwa saboda halin da sauran mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kadunan ke ciki a daji bayan kwashe watanni hudu.

Sakin wadannan mutane uku dai ya kai adadin wadanda aka sako zuwa mutane 23 sai dai kuma yanzu tattaunawar sakin mutanen ta koma tsakanin 'yan-bindigan da kuma iyalan wadanda ke hannun su a dajin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG