Jama’a masu zaman jiran sakamakon zaben da aka gudanar ne jiya Asabar 25 ga Fabrairun 2023.
Shugaban Amurka Joe Bide ya ce ya yaba wa yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a Najeriya, da ta samu sanya hannun jami’iyyun siyasa da ‘yan takara da zasu fafata a zaben shugaban kasar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jakadan kasar Canada a Najeriya Mr. Jammie Christoff ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a wani taron hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasar ta Canada, don karfafa matakan hadin kai na tunkarar kalubalen safarar mutane da yin kaura ba bisa ka’ida ba.
Taron na manyan Hafsoshin Sojojin da sauran shugabannin hukumomin tsaron kasar na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Boko Haram suka saki wani faifan Video wanda a ciki suke barazanar kawo cikas yayin zaben.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata labarin cewa ya umarci bankuna a kasar da su fara karbar takardun kudi na Naira dari biyar da Naira dubu daya.
Shuganan hukumar zaben Najeriyar ya bayyana cewa tun a watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne suka fidda wasu jerin ababe guda goma sha hudu da bisa doka dole sai an kaddamar dasu don tabbatar da ingancin zaben
An fara samun karin bayani game da mummunan farmakin da jiragen yakin mayakan saman Najeriya suka kai a sansanin mayakan Boko Haram dake dajin sambisa da safiyar yau asabar, inda suka babbake sansanin biyo bayan ruwan boma bomai da rokoki.
“Amurka ta ce ba ta goyon bayan kowane ‘dan takara a zaben Najeriya. Ta ce ita dai babban muradinta shi ne ta ga an gudanar da ingantaccen zabe, na gaskiya mai cike da adalci, wanda kowa da kowa zai na'am da shi”
“Ana dai zargin sojojin da danne hakkin dan Adam ciki har da zubar da cikin mata fiye da dubu goma da ake zargin Boko Haram sun yi wa Fyade”
Wani bene mai hawa uku ya ruguje a unguwar Gwarinpa da ke Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya.
Wata babbar kotu a birnin Kaduna ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato DSS da ta gaggauta gurfanar da mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu a gaban kotu.
Birgediya Janaral Tukur Isma'il Gusau, sabon kakakin hedikwatar rundunar tsaron Najeriya, ya amshi ragamar aiki daga hanun darakta mai barin gado, Manjo Janaral Jimmy Akpor.
A kokarin kawo karshen aika aikar 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a yankunan kasashen tafkin Tchadi, dakarun kawancen kasashen yankin na can na ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan a baki dayan yankin cikin wani farmaki ba kakkautawa da ma sintiri da ake yi akai akai.
Hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara wani shirin horas da kwamandojin rundunoninta na kwantar da tarzoma su saba'in da tara don tabbatar da zama cikin damara kafin lokaci da bayan babban zaben gama gari na kasa da za'ayi cikin wannan shekara.
Biyo bayan shafe fiye da shekara daya da rabi da daliban kwalejin gwamnatin Tarayya su ke hanun yan bindiga dadi a cikin aji, yanzu dai matsalar ta dauki wani sabon salo.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato DSS, ta ce bata wani yunkuri don cafke shugaban hukumar zaben kasar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu
Hukumar tsaron DSS ta Najeriya ta ce jami'anta sun damke wasu ‘yan ta'adda da suka kitsa kai harin ta'addanci a kusa da fadar mai martaba Ohinoyi na masarautar Igbira da ke yankin karamar hukumar Okene a jihar Kogi a daidai lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ziyarar aiki a yankin.
Hedikwatar Rundunar sojojin saman Najeriya ta tabbatar da cewa jiragen yakinta sun kai wani mummunan farmaki akan gomman mayakan yan ta’addan Boko Haram inda ta hallaka su da da daman gaske.
Yayin wani farmakin da sojoji na musamman daga sashi na 171 da mayakan saman Najeriya, su ka kaddamar kan wani sansanin barayin daji, an sami nasarar ceto wasu yan kasar China 7 da ake garkuwa da su.
Cikin sanarwar da ya sanyawa hannu, kakakin hedkwatar rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Jimmy Akpor ya ce, akwai tukwicin Naira miliyan biyar da aka sanya ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga kama daya daga cikin ‘yan bindigar.
Domin Kari